1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libya ta yi watsi da sukar da kasashen duniya ke ma ta game da hukuncin kisan nan

December 20, 2006
https://p.dw.com/p/BuX2

Kasar Libya ta ce ba zata saduda da matsin lamba daga kasashen duniya game da hukuncin kisan da aka yankewa wasu nas-nas ´yan Bulgariya su biyar da kuma wani likita Bafalasdine ba. wata kotu a birnin Tripoli ta yanke musu wannan hukunci bayan ta samesu da lafin yiwa kananan yara ´yan kasar ta Libya allurar kwayoyin cutar HIV. Kasashen duniya sun tir da hukuncin kotu. A tsawon shekaru 7 da suke tsare, dukkan ma´aikatan jiyya da kuma likitan dan Falasdinu sun sha nanata cewa ba su aikata laifi ba. alkalan kotun sun yi fatali da shaidar da aka bayar da ke nuni da cewa annobar HIV din da ta shafi yaran kimanin 267 a wannan asibiti, ta fara tun gabanin isar mutanen a Libya a shekara ta 1998. Masana ilimin kimiyya na kasar Birtaniya sun ce rashin tsabta a asibitin ya janyo wannan annoba.