1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Likitoci na binciken musabbabin mutuwar Milosevic

March 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5H

Likitoci a birnin Hague sun fara bincike a kan gawar tsohon shugaban kasar Serbiya Slobodan Milosevic domin gano musabbabin mutuwar sa. Milosevic ya rasu a ranar Asabar din da ta wuce a gidan wakafi inda yake jiran hukunci a kotun kasa da kasa ta majalisar dinkin duniya a dangane da tabargaza ta kisan kare dangi. Kwararrun likitocin sabiya zasu gudanar da binciken. Iyalan Milosevic da magoya bayan sa sun zargi kotun ta kasa da kasa da alhakin mutuwar Milosevic. A watan da ya gabata Kotun ta ki amincewa da bukatar Milosevic wanda ke fama da hawan jini da ciwon zuciya, na barin sa ya je a duba lafiyar sa a wani asibiti a kasar Rasha. Mutuwar Milosevic ta haifar da damuwa daga iyaye da matan wadanda aka yiwa kisan gillar a Sebrenica, na rashin fuskantar hukunci. Milosevic mai shekaru 64 da haihuwa na fuskantar tuhumar kisan gilla da aka yiwa musulmi 8,000 a garin Sebrenica a shekarar 1995. Tun a shekarar 2002 ake tsare da shi inda yake fuskantar tuhuma akan laifuka har guda 60 na take hakkin bil Adama a lokacin yakin Balkans a shekarun 1990.