1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

LIKITOCIN SOJIN GONA A KASAR SALIYO

February 26, 2004
https://p.dw.com/p/Bvlg

Bisa wan nan lamari a yanzu haka gwamnatin kasar ta fara kaddamar da wani gagarumin kamfe na yadda za,a wayarwa da mutane kai kann sojojin gona a fannin aikin likitan tare kuma da cafke su don gurfanar dasu a gaban kuliya. Wan nan dai kamfe a cewar majiya mai karfi daga kasar ta saliyo, za,a fadada ta har ya zuwa lungu lungu da sako sako na fadin kasar baki daya,don tabbatar da cewa babu wani likita sojin gona dake gudanar da wan nan aiki na likitanci. Rahotanni dai sun shaidar da cewa don cimma wan nan buri tuni kungiyyar maikatan aikin likita ta kasar ta hada karfi da karfe guri guda da gwamnatin kasar don aiwatar da wan nan gagarumin aikin a fadin kasar baki daya. A yanzu haka dai rahotannin sun shaidar da cewa jamian tsaron kasar ta Saliyo na tsare da likitoci na sojin gonar da yawan su ya kai guda ashirin da biyar.

A kuwa ta bakin wani dalibi dake karatu a tsangayar aikin lafiya ta jamiar kasar ta saliyo Ebie Cole, cewa yayi likitocin sojin gonar na gudanar da wan nan aikin ne bisa irin rashin ilimi da yayiwa da dama daga cikin mutanen kasar katutu. Bugu da kari a cewar dalibi Cole, likitocin sojojin gonar sun samu damar sakin jikin su don gudanar da wan nan aikin ne bisa yakin basasa da kasar ta fuskanta a shekara ta 1990,wanda a lokacin ba a bada muhimmanci so sai a kansu ba na maganin su daga cikin alumma.

A hannu daya kuma maikatar lafiya ta kasar ta tabbatar da cewa anyi asarar rayukan mutanen kasar da daman gaske sakamakon irin wan nan aiki na likitocin sojojin gonar.

Amma abin bakin ciki a cewar maikatar shine da dama daga cikin wadan da aka cafke na yin wan nan mummunar sana,ar masu nuna nadama ba kann irin halin kaka ni kayi da suka tsumduma iyaye da yaya na wasu mutanen kasar. A misali Musa Conteh mai shekaru 40 dake zaune a arewacin kasar ta saliyo ya shaidawa kamfanin dillancin labaru na Ips cewa yana yin wan nan sana,a ne ta likitan sojin gonar don ciyar da yayan sa 10 a hannu daya kuma da tallafawa magabatan sa da yan uwan sa. Shi kuwa Sorie Kanu cewa yayi ya tsunduma ne a cikin sana,ar don tallafawa mutanen kauyen su,domin a cewar sa mutanen kauyen nasu na fama da matsaloli na karancin likita.

Bugu da kari Mr Sorie ya tabbatar da cewa a tun lokacin daya fara wan nan sana,a babu wani mara lafiya daya taba mutuwa a hannun sa sakamakon bashi magani daya yi. A waje daya kuma bayan kokarin da kungiyyar likitoci da kuma gwamnatin kasar keyi na samo bakin zaren warware wan nan matsala, a yanzu kuma rukunan guda biyu rahotanni sun shaidar da cewa sunyi nisa game da laluben magungunan da suka baci ake kuma sayarwa don lalata su,a hannu daya kuma da cafke ire iren mutanen dake dillancin su. Ibrahim sani.