Littafin adabin baka na Hausa
March 27, 2009Talla
A kwanakin baya aka yi bukin ƙaddamar da wani littafi kan waƙoƙin baka na Hausa a jami´ar Bayero dake birnin Kano.
Shi dai wannan littafi wanda Farfesa Sa´idu Mohammed Gusau na cibiyar koyar da harsunan Nijeriya a jami´ar ta Bayero ya wallafa, ya ƙunshi muhimman fannoni na rayuwar Bahaushe da suka haɗa da ita kanta ƙasar Hausan da sarakunanta da halaiya da nau´o´in waƙoƙin baka na Hausa da kiɗa na Hausawa da kuma kayan yin su. An bayyana wannan littafi da cewa zai ba da babbar gudunmawa ga harshen da kuma al´adun su kansu Hausawa.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal