1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

240709 Dialog Muslimischer Friedhof Wien

September 4, 2009

Tun fiye da shekaru bakwai da suka wuce ƙungiyar musulmai a ƙasar Austriya suka fara tattaunawa da hukumomin birnin Vienna don samun izinin gina maƙabartarsu kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

https://p.dw.com/p/JQlS
Hoto: Nikos Pilos

Bayan muhawwarori da shugabannin siyasa, jinkiri saboda durƙushewar kamfanin gine-gine da kuma adawar da wata ƙungiyar mazauna yankin Vienna ta nuna ga shirin gina maƙabartar, yanzu dai haƙa ya cimma ruwa, domin birnin Vienna da ma ƙasar Austriya baki ɗaya sun samu maƙabartar musulmi ta farko. Tun a cikin tsakiyar wannan shekara aka fara yiwa musulami jana´iza a wannan maƙabarta. Hakan dai na da muhimmanci ga iyalan mamatan domin suna iya kai ziyara maƙabartar domin yi musu addu´o´i.

Kamar yadda wataƙila kuka ji a shimfiɗar shirin a yau dai za mu yada zango ne a birnin Viennan na ƙasar Austriya inda al´umar a karon farko al´umar musulamin wannan yanki suka samu izinin gina maƙabartar kansu. Wannan maƙabartar ta musulmi an gina ta a wata unguwar masana´antu dake wajen birnin na Vienna. An ƙawata ƙofarta da ayoyin Al-Qur´ani mai girma. Sannan a dab da wurin ajiye motoci ana iya hango wani gini mai kubba irin ta masallaci to sai dai ba ya da hasumiya. Ana yiwa mamatan Sallah dab da kabarin, inji Kadir Eükoglu ɗaya daga cikin masu ɗaukar nauyin yiwa mamata jana´iza a maƙabartar.

“Ga musulmai a Austriya wannan karamcin na da alfanu da yawa. Wannan maƙabartar ta mu ce kuma muna ji tamkar a gida muke musamman a dangane da rufe mamatanmu. Akwai ɗakunan wanka, da wuraren sallah kana kuma ƙaburburan na fuskantar alƙibla kamar yadda shari´a ta yi umarni. Ba zamu taɓa mantawa da wannan damar da hukumomin birnin Viennan suka bamu ba.”

Maƙabartar dai tana a bayan ɗakin da aka tanadar don sallah, kuma girmanta ya kai girman filin wasan ƙwallon ƙafa. Tun a gaba dai an tone ƙaburbura masu tazarar ƙafa ɗaya da rabi da juna. An yiwa ko-wane alama da kuma sunan mamaci akan wani ƙaramin katako. A kwanakin baya wata da ake kira Fidan Dilek daga ƙasar Turkiya ta binne mahaifinta. Ta yaba da irin karamcin da kuma tarba da masu kula da maƙabartar suka yi mata.

“Na gamsu matuƙa da wannan hukumar gudanarwa ta maƙabartar. Sun yi min kyakkyawar tarba kana kuma sun yi min bayani dalla-dalla kan yadda za a tafiyar da jana´izar. Ba da wata-wata ba sun samo min kamfanin da zai taimaka wajen yiwa mahaifina jana´iza. A nan dai na ji daɗi ƙwarai da gaske.”

Kamfanin shirya jana´izar ne ya tafiyar da dukkan abubuwan da suka wajaba, kama daga na hukuma da neman lokacin yin jana´iza, da yiwa gawar wanka da yi mata salla da kuma binneta gaba ɗaya. Wannan ɗawainiyar dai ta ci kuɗi euro 3500, amma in da Fidan ta kai gawar mahaifinta Turkiya da abin da za ta kashe ya ninka wannan adadin har sau uku.

Kawo yanzu duk wanda ke son ƙaurcewa kai gawar mamacinsa gida, ana rufe su ne a babbar maƙabartar birnin Vienna inda tuni ta cika kuma a dole ake binne gawawwaki kan wasu. Hakazalika ba a iya yin wasu abubuwan kamar yadda addini ya tanada. Muhimmin abu ga jana´izar musulmi dai shi ne yiwa gawa wanka da binne ta tana fuskantar alƙibla. Sharaɗi guda ɗaya da ba a iya cikawa har yanzu a Austriya shi ne binne gawa ba a cikin akwati ba, inji Mouda Kouja na gamaiyar musulman Austriya“Bisa dokokin ƙasar Austriya, ba a yarda a binne wata gawa ba tare da an saka ta cikin akwati ba. Wato abin nufi dokokin maƙabarta sun tanadi yin amfani da akwatin gawa, ko an ƙi ko an so. A saboda haka a ɓangarenmu mun nemi bayanai daga manyan malaman addini ko wannan doka ta musamman ka iya aiki kanmu a matsayin wani abin da masu iya magana kan ce da babu gyara ba daɗi.”

An ɗauki tsawon shekaru bakwai kafin a kai ga samun maƙabartar musulmi ta farko a Austriya. Da farko wata ƙungiyar mazauna yankin Vienna da masu matsanancin ra´ayin ƙyamar baƙi sun hana majalisar dokoki ba da izinin gina maƙabartar. Sannan daga bisani kamfanin da aka bawa ƙwagilar aikin ginin ya durƙushe. To amma yanzu duk waɗannan sun zama tarihi bisa namijin ƙoƙarin da gamaiyar musulman Austriya wadda aka kafa ta tun a shekarar 1979 ta yi, inji Moudar Kouja sannan sai ya ƙara da cewa.

“An tabƙa muhawarori da dama. Alal misali wata ƙungiya dake samun goyon bayan jam´iyar FPÖ, amma hankali ya kwanta bayan da ´yan wannan yankin suka ga aikin ginin maƙabartar da muke yi. A ƙarshe sun ga yadda muka ƙawata ginin da harabarsa, wato abin da ba a taɓa samu ba a da.”

Mahaifin Fidan Dilek na ɗaya daga cikin musulmin da aka rufe a sabuwar maƙabartar musulmin ta Vienna. A matsayinsa na shugaban ƙawancen manyan kantuna mahaifin na ta sananne ne a tsakanin gamaiyar Turkawa a Austriya. Labarin cewa za a yi masa jana´izar a Vienna maimakon a Turkiya ya bazu tamkar wutar daji, inji Fidan Dilek.

“An yi ta wannan tambayar ce, domin kawo yanzu ba a saba yiwa ´yan Turkiya jana´iza a nan ba, sai wanda bai da iyali ko mara gata. Ana yawaita tambayar yadda ake jana´iza a nan. Duk waɗanda suka halarci wannan jana´iza sun gamsu, musamman ma ´yan uwansa. Hakan ya kasance muhimmin abu gare ni.”

Wakilan gamaiyar musulman Austriya na masu ra´ayin cewa maƙabartar na matsayin wata hanya ta kyatatuwar zamantakewa, domin yanzu ana iya rufe musulman a wuraren da suka yi zama, kamar yadda yanzu suka yaɗu ko-ina a cikin Turai. Suka ce maƙabartar kyakkyawar shaida ce cewar sannu a hankali an fara ganewa da ainihin halin da ake ciki.

Mawallafa: Emir Numanovic/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadisou Madobi