1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ma'aikata Baki A Jamus

September 2, 2004

A bayan yakin duniya na biyu Jamus ta nemo ma'aikata baki daga kasashen ketare domin su cike gibin da take fama da shi na ma'aikata tare kuma da taimakawa wajen sake gina kasar, wacce yaki yayi kaca-kaca da ita

https://p.dw.com/p/Bvgm

A daidai ranar 10 ga watan satumban shekarar 1964 aka gabatar da wani kasaitaccen bikin marhabin lale da wani dan kasar Portugal mai suna Amando Sa Rodrigues, wanda a wancan lokaci ya kasance cikon miliyan daya a tsakanin ma’aikata baki #yan ci rani da suka shigo Jamus, aka kuma yi masa kyautar babura. Wannan labarin kuwa duk wanda ya ji shi sai ya shiga mamaki da tu’ajjabi a game da cewar Jamusawa sun karbi rukunin farko na ‚yan ci ranin da hannu biyu-biyu. An saurari irin wannan bayanin daga wani da ake kira Konstantin Kalandranis dake da shekaru 53, wanda kuma ya shigo Jamus a shekarar 1962 yana dan shekaru 11 da haifuwa. Mahaifinsa ya kasance daga cikin rukunin ‚yanci rani na farko-farko da suka shigo Jamus daga kasar Girka. Ya ce daga cikin wadanda suka hallara a tashar jiragen kasa domin yi musu marhabin har da shugaban kamfanin da mahaifinsa yayi wa aiki. Amma matsalar farko da suka fuskanta ita ce ta yare saboda babu daya daga cikin danginsa dake jin Jamusanci. Ya zama wajibi akansa ya sake fara makaranta daga tushe saboda rashin kwarewa a harshen Jamusanci. To sai dai kuma duk da wannan matsala ta yare ma’aikata ‚yan ci rani sun ci gaba da tuttudowa zuwa Jamus daga kasashen Italiya da Spain da Portugal da Yugoslabiya da Girka da kuma Turkiyya, domin cin gajiyar bunkasar tattalin arzikin da Allah Ya fuwace wa Jamus. A tsakanin 1960 zuwa 1972 an samu bunkasar yawan ma’aikata baki daga kashi daya da digo biyar zuwa kashi goma da digo takwas a tsakanin illahirin ma’aikata dake nan kasar. Wato dai a takaice a shekarar 1960 duka-duka yawan ma’aikata bakin bai wuce mutum dubu 330 ba, amma adadin ya karu zuwa ma’aikata miliyan daya da dubu dari biyar a shekarar 1969 sannan ya zarce zuwa miliyan biyu da dubu dari shida a shekarar 1973. An dakatar da debo ma’aikata ‚yan ci rani daga ketare ne sakamakon rikicin man fetur da aka fuskanta a 1973. To sai dai kuma abin mamaki, bisa sabanin yadda Jamusawa suka tsammata, wadannan ‚yan ci rani sun share wuri ne suka ci gaba da zamansu a nan kasar a maimakon komawa gida bayan aiki na dan gajeren lokaci. Shi kansa Konstantin Kalandranis dan usulin kasar Girka, bayan da tafiya tayi tafiya ya samu kwarewa a harshen Jamusanci ya kuma, inda ya wayi gari a matsayin injiniya dake aiki a kamfanin sarrafa motocin Ford dake birnin Kolon. Kuma ko da yake ba ya rike da takardar fasfo ta Jamus, amma Kalandranis ya ce ba ya fuskantar wata matsala a rayuwarsa ta yau da kullum. ‚Ya’yansa guda uku, duk a nan Jamus aka haifesu suka taso suka kuma koyi sana’o’i na hannu. Ya ce bayan sama da shekaru arba’in na rayuwa a nan kasar tuni Jamus ta zame masa gida. Ainifin matsalar da kan hana ruwa gudu wajen cude-ni-in-cude-ka tsakanin Jamusawa da takwarorinsu ‚yan kaka-gida shi ne yawa-yawancin bakin ba sa hulda da Jamusawan kai tsaye. Da zarar sun wayi gari sai su kama hanyarsu ta zuwa aiki daga can kuma ko dai su dawo gida ko kuma su karasa zuwa cefane. Abu mafi alheri kamar yadda wani dan usulin kasar Italiya da ake kira Rocco ya nunar, shi ne karfafa tuntubar juna tsakanin bangarorin biyu.