1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ma'aikatan jiyyan Bulgaria sun kama hanyar zuwa gida daga Libya

July 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuFf

Jamian kula da lafiyar nan shida da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai a kasar Libya bisa laifin yiwa yara kanana 400 allurar kwayar cutar HIV sun kama hanyarsu ta zuwa gida Bulgaria.An samu wannan ci gaba ne bayan tattaunawar jiya a Libya tsakanin Kungiyar Taraiyar Turai tare da goyon bayan uwargidar shugaban Faransa da kuma gwamnatin Libya.

Gidan rediyon kasar Bulgaria ya bada rahoton cewakomishinar kula da harkokin wajen KTT Benita Ferrero Waldner take rakiyar wadannan maaikatan jiyyan 5 da likita guda wadanda suke gidan yari tun 1999 bayan yanke masu hukuncin kisa.

Sai dai kuma a makon daya gabata majalisar koli ta sharia ta Libya ta mayarada hukuncin zuwa daurin rai da rai.

A halinda ake ciki dai Faransa da KTT sunyi maraba da sakin jamian.

Sanarwa da aka fitar a Brussels tace shugaban Faransa da hukumar turai sunyi maraba da wannan jin kai da Libya ta nuna kuma sun sadaukar da kansu ga taimakon yara dake dauke da cutar AIDS.