1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ma´aikatan sufuri a New York sun kawo karshen yajin aiki

December 23, 2005
https://p.dw.com/p/BvFO

Ma´aikatan sufurin jama´a a birnin New York sun kawo karshen yajin aikin da suka shafe kwanaki 3 suna yi, to amma jami´ai sun ce za´a dauki tsawon sa´o´i 24 kafin komai ya dawo yadda aka saba. Shugabannin kungiyar ´yan kwadago ta ma´aikatan sufurin suka amince da dakatar da yajin aikin a wani kuri´a da suka kada. Shugabannin dai na fuskantar tara da kuma barazanar hukunci dauri a gidajen maza. A halin da ake ciki hukumar sufurin ta birnin New York ta yi karin tayin ta na albashin ma´aikata to amma ta ce dole ne ma´aikatanta kimanin dubu 34 su kara yawan gudummawar da suke bayar a fannin fansho. Magajin garin New York Michael Bloomberg ya ce yajin aikin ya yiwa tattalin arzikin birnin mummunan lahani. Jami´ai sun ce yajin aikin ya janyo asara kudi kimanin dala miliyan dubu daya ga kantuna da giajen wasannin kwaikwayo da kuma wuraren cin abinci.