1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace mafi kudi a Duniya

Abba BashirSeptember 25, 2006

Bayani akan Mace mafi kudi a Duniya

https://p.dw.com/p/BvVE
Oprah Winfrey
Oprah WinfreyHoto: AP

Jamaa masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na wasikun ma su sauraro,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fitone daga hannun malama Yahanasu Yusufu, Mirya, Jamhuriyar Niger. Malamar tana tambaya ne akan cewa; wace mace ce ta fi kudi a Duniya?

Amsa: To bincike ya tabbatar mana da cewa , a bayanai na baya bayannan, mata biye ne a halin yanzu suke rike da wannan kambu, kuma dukkanin su suna da dangantaka da juna.

Tafarko ita ce Alice Walton “yar shekaru 56 da haihuwa, kuma “ya ce ga Wal Mart, wanda ya kafa kamfanin Sam Walton. An dai kiyasta cewa tana da avalla Dalar Amurka Miliyan dubu 18.Kuma tana zaune ne a Jihar Texas, ta Kasar Amurka.

Dayar kuwa ita ce Helen Walton “Yar shekara 85 da haihuwa, wato tsohuwar matar Sam, kuma ita ma an kiyasta kudinta da akalla Dalar Amurka Miliyan dubu 18. Tana zaune ne a Bentonville, na Jihar Arkansas a dai Kasar Amurkan.

Madam Liliana Bettencourt, ita ce mace ta biyu a jerin sunayen mata mafi kudi a Duniya, kuma Diya ce ga L’Oreal mai kamfanin Eugene Schueler. An kiyasta cewa tana da yawan kudin da suka kai dalar Amurka Miliyan dubu 17,200. Yanzu haka dai tana zaune ne a Kasar Faransa.

A takaice dai kididdiga ta tabbatar da cewa, Mutane tara daga cikin mutanen da suke a rukuni na biyar na wadanda suka fi yawan kudi a Duniya, Mata ne.

Mace mafi kudi a Duniya a cikin wadanda suka nemi kudi da gumin su, ba wai ta hanyar gado ba, ita ce Madam Rosalia Mera, mai shekaru 61 da haihuwa wadda aka kiyasta cewa tana da kudin da yawan su yakai dalar Amurka Miliyan dubu biyu. Tun asali wannan mata dai ta fara ne da sana’ar Tela, inda take dinka situru a cikin gidan ta. Daga baya ta habaka har ta kai ga bude anfani.

Madam Oprah, ita ce bakar mace mafi kudi a Duniya, kuma a yanzu haka ta bude wani asusu na tallafawa matasa musamman ma mata a Nahiyar Afirka. Tana da kudin da aka kiyasta yawan su da cewa sun kai kimanin Dalar Amurka Miliyan 1,300.