1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace ta zama Babbar alkalin kotun kolin Brazil

Zainab A MohammadMarch 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bu7N

BRAZIL

A karo na farko cikin shekaru 115 da kafuwarta, kotun kolin kasar Brazil ta samu mace a matsayin babbar Alkali.A daren jiya nedai kotun ta gudanar da kuriar raba gardama,wanda ya bawa Justice Ellen Gracie Northfleet ,mai shekaru 58 da haihuwa nasarar maye gurbin Justice Nelson Jobin,a matsayin babbar Alkali.Bisa tsarin kasar dai zata kasance shugabar janhuriyar mai rikon gado ,bayan mataimakan shugabannin majalisun kasar biyu.Ayayinda take a matsayin alkali a wannan kotu dai Justice Ellen ta taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da ayyukanta ,tare da marawa gwamnati baya dangane da harkokin kudi,musamman wajen biyan basussukanta.A ranar 30 ga wannan wata nedai Justice Ellen zata haye mukamin babbar Alkalin kotun kokin kasar.A karshen shekarar data gabata nedai tsohon Alkalin kotun ya sanar da yin Murabus daga jagorancin kotun kolin Brazil din.