1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace ta zama firaminista a Australiya

June 24, 2010

Australiya ta zabi mace a mukamin firaminista a karon farko.

https://p.dw.com/p/O1TX
Hoto: AP

A karon farko cikin tarihinta, Australiya ta amince wata mace ta rike mukamin firaministan biyowa bayan murabus da shugaban gwamanti wato Kevin Rudd yayi. Majalisar dokokin kasar ta kada kuriar amincewa da Julia Gillard , tsofuwar lawya mai shekaru 48 da haihuwa a mukamin firamista ta riko.

Kevin Rudd ya ajiye aikinsa sakamakon suka da ya ke ta sha game da kamun ludayinsa shekaru biyu da kuma watanni bakwai bayan kama aiki. Jullia Gillard ta yi alkawrin shirya sabon zabe cikin yan watanni masu yuwa.

Mawallafi. Mouhamadou Awal

Edita. Umaru Aliyu