1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Macron: A kawo karshen mamayar yankin Falisdinawa

Ramatu Garba Baba
December 10, 2017

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya shawarci Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ke ziyarar aiki a kasar da ya yi taka tsantsan wajen daukar mataki kan rikicin yankin.

https://p.dw.com/p/2p7A9
Frankreich Paris Emmanuel Macron und Benjamin Netanjahu
Hoto: picture-alliance/E. Blondet

Macron ya ce akwai yiyuwar sake komawa teburin sulhu kan magance rikicin yankin in har an bi a hankali. Macron a jawabinsa a yayin ganawa da Neatanyahu ya soma da yin alla-wadai da rikicin da ya kunno kai a 'yan kwanakin nan a sanadiyar mataki shugaban Amirka Donald Trump kan mayar da Kudus babban birnin kasar Isra'ila.

Shugaban ya jaddadawa Netanyahu kan daukar mataki na kawo karshen mamayar da Isra'ila ke yi a yankin Falisdinawa, abinda ya ce zai kasance ginshiki a kokarin da ake na ganin an samar da zaman lafiya a yankin, Macron ya kara da cewa akwai bukatar yin nazari cikin tsanaki kan tatauna makomar yankin.

Kungiyar hadin kan kasashen Larabawa a na ta bangaren kira ta yi ga Amirka da ta soke matakin bayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar isra'ila. Ministocin harkokin kasashen waje na kungiyar ne suka yi wannan kira a wata sanarwa da suka fitar da safiyar wannan Lahadi a karshen taron da suka gudanar a birnin Alkahira na kasar Masar, inda suka yi kira ga kasashen duniya da su bijire bisa matakin kasar ta Amirka.Shugaban Masar Abdelfatah al-Sisi ya mika goron gayata ga shugaban Falisdinawa Mahmoud Abbass don tattauna matakin na Trump.