1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Macron ya kafa sabuwar gwamnatin Faransa

Yusuf Bala Nayaya
May 17, 2017

Fitaccen dan gurguzun nan Jean-Yves Le Drian na a matsayin wanda zai jagoranci harkokin kasashen wajen Faransa.

https://p.dw.com/p/2d733
Emmanuel Macron Paris
Hoto: Reuters/G.Fuentes

Sabon Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kafa gwamnati a karon farko a wannan rana ta Laraba inda ya bayyana fitaccen dan gurguzun nan Jean-Yves Le Drian a matsayin wanda zai jagoranci harkokin kasashen waje da 'yar majalisa daga Kungiyar Tarayyar Turai Sylie Goulard a matsayin ministar tsaro.

Wasu manyan jami'ai da aka nada sun hadar da magajin garin birnin Lyon Gerard Collomb a matsayin ministan harkokin cikin gida sai mai matsakaicin ra'ayi Francois Bayrou da zai kula da harkokin shari'a, da mai ra'ayin rikau Bruno Le Maire da aka bayyana a matsayin ministan tattalin arziki.