1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Madugun adawar KwangoTshisekedi ya rasu

Salissou Boukari
February 2, 2017

Allah ya yi wa babban dan adawar nan na kasar Kwango Etienne Tshisekedi rasuwa da yammain ranar Laraba (01.02.2017), a wani asibiti da ke birnin Brussels na kasar Beljiyam.

https://p.dw.com/p/2WpUg
Kongos Tschisekedi ist nach Kinshasa zurückgekehrt
Marigayi Etienne Tshisekedi lokacin da ya zo kasar ta Kwango a ranar 27 ga watan Yuli na 2016 tare da magoya bayansaHoto: picture-alliance/AP Photo/P Photo/J. Bompengo

Lokacin da suka samu labarin mutuwarsa, da dama daga cikin 'yan kasar ta Kwango da ke birnin Brussels sun je asibitin Elizabet inda ya rasu, kuma Janu Kabuya na daya daga cikin 'yan gogormayawar kasar ta Kwango da ke zaune a kasar ta Beljiyam da suka je asibitin inda yake cewa:

"Muna cikin babban bakin ciki, domin marigayi Étienne Tshisekedi ya kasance wani gimshiki na kokowar wanzar da demokaradiyya a kasar Kwango."

Marigayin wanda ya mutu ya na da shekaru 84 a duniya, ya yi suna a gwagwarmayar da ya yi tun a lokacin mulkin tsohon dan kama karya Mobutu Seseseko, kafin ya kasance dan adawa na kullun a kasar.

Labarin mutuwar ta shi dai ya girgiza al'ummar kasar ta Kwango, musamman magoya bayansa da ke jam'iyyarsa ta UDPS da sauran gungun 'yan adawan kasar.