1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Madugun 'yan tawayen Sudan ya fatattali manyan kwamandojinsa

Suleiman BabayoJuly 22, 2015

An samu rarrabuwa tsakanin 'yan tawayen Sudan ta Kudu da ke fafatawa da gwamnati abin da zai kara zafafa yakin basasan kasar

https://p.dw.com/p/1G2e9
Südsudan Rebellenführer Riek Machar
Hoto: picture-alliance/AP Photo/K. Senosi

Jagoran 'yan tawayen kasar Sudan Kudu Riek Machar ya fatattali biyu daga cikin manyan kwamandojin sojin rundinar da yake shugabanci, abin da ke nuna sabani tsakanin mayakan 'yan tawayen, tare da raunana duk wata yarjejeniyar neman zaman lafiya da gwamnati.

'Yan tawayen sun ce an kori Maja-Janar James Gadet mataimakain kwamnan mayakan sa-kai, Gadet yana karkashin takunkumi kasashen Turai da Amirka, sannan kuma an kori Maja-Janar Gathoth Gatkuoth mataimakain babban habsa mai kula da ayyuka.

Yakin basasan Sudan ta Kudu ya balle a watan Disamba na shekara ta 2013, lokacin da Shugaba Salva Kiir ya zargin tsohon mataimakinsa Riek Machar da yunkurin kifar da gwamnati. Tuni rikici ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane, sannan ya raba fiye da mutane milyan biyu da gidajensu.