1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahaukaciyar guguwa ta yi kisa a Dominika

Abdourahamane HassaneAugust 29, 2015

Mutane 20 ne guguwar ta kashe yayin da gidaje da gadoji da hanyoyin mota da dama sun lalace. Wasu jama'ar dubu 150 suka rasa wutar lantarki a Jamhuriyar Dominika.

https://p.dw.com/p/1GNic
Dominikanische Republik Sturm Erika
Hoto: Reuters/R. Rojas

Mahaukaciyar guguwa haɗe da ruwan sama da iska mai karfin gaske wadda ta ratsa ƙasar Haiti ta kashe mutane 20 a tsibirin Dominika yayin da wasu da dama aka rasa inda suke ,Roosevelt Skerrit wanda shi ne firaministan ƙasar, ya ce ''Ina cikin damuwa da ɓacin rai sossai a wannan jawabi da nake yi zuwa gareku a sakamakon wannan bala'i da ya faɗa wa ƙasarmu,dole sai mun nuna dangana da kuma yin juriya.''


Ruwa kamar da baƙin ƙwarya da aka riƙa sheƙawa ya haddasa ambaliya tare da zubar laka wacce ta bizne wasu mutanen da ransu. A halin da ake ciki hukumomi sun taƙaita zirga-zirgar jama'a kana, sannan kuma an rufe makarantu tare da haramtawa jiragen ruwan motsawa daga bakin teku.