1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahaukaciyar guguwar Dean ta rage ƙarfi

August 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuDa

Mahaukaciyar guguwar nan mai suna Dean na ci gaba da hadasa ta´adi, a duk yankunan da ta ratsa.

A yau ta darkaka zuwa ɓangaren kudu na gaɓar tekun Mexico, inda ta jawo asara mai tarin yawa, duk da matakan riga kafi, da hukumomi su ka ɗauka.

A yankin Puerta Bravo gwamnatin ƙasar Mexique ta kafa dokar ta ɓace, tare da rufe filayen saukar jiragen sama da hanyoyin zirga zirgar motoci da jiragen ƙasa.

Kazalika ta tura sojoji 2000 da yan sanda kimanin dubu ɗaya, domin agazawa jama´a.

A yan kunan da ta rasta, mahaukaciyar guguwar Dean, ta yi sanadiyar ambaliyar ruwan teku, wanda su ka ci gidaje da rayuka masu yawa.

To saidai ya zuwa yanzu masana harakokin kaɗawar iska, sun bayyana cewar, ƙarfin guguwar ta Dean ya ragu daga 5 zuwa 3, a ma´aunin iska na Saffir- Simpson, wato daga kilomita 230 ko wace awa, zuwa kilomita 178.