1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahawara a majalisar Birtaniya kan ficewa daga EU

Gazali Abdou Tasawa
February 1, 2017

Majalisar dokokin Birtaniya na mahawara kan bai wa gwamnatin kasar hurumin soma tattaunawa da EU kan batun ficewar kasar daga cikin kungiyar.

https://p.dw.com/p/2Wlbc
Großbritanien Britisches Parlament beginnt mit Debatte über Brexit-Gesetz | David Davis
David Davis mai kula da aiwatar da shirin ficewar Birtaniya daga EU lokacin mahawara a majalisar dokoki da ke birnin LondonHoto: picture alliance/dpa//PA Wire

A wannan Laraba 'yan majalisar dokokin Birtaniya za su ci gaba da mahawarar da suka soma a ranar Talata kan kudirin dokar da zai bai wa gwamnatin kasar hurumin kaddamar da tattaunawa da kasashen Turai kan aiwatar da matakin ficewar kasar ta Birtaniyar daga cikin Kungiyar EU.

'Yan majalisar dokokin Birtaniyar sun dai share yinin ranar Talata suna zazzafar mahawara inda masu adawa da matakin ficewar Birtaniyar daga cikin EU, suka yi kokarin kawo cikas ga kudirin dokar. Sai dai da yake jawabi a gurin bikin bude zaman mahawarar, ministan kula da aiwatar da shirin ficewar Birtaniyar daga EU, David Davis ya ce ba bu ja da baya kan wannan batu inda ya yi karin bayani yana mai cewa:

"Ba wai kudirin doka ba ne na sanin ko Birtaniya za ta fice daga cikin EU ko kuma a'a ba, ko kuma ma ta yaya za ta fice. Abin da ya kawo mu kawai shi ne aiwatar da mataki wanda tuni 'yan kasa suka amince da shi kuma bakin alkalami ya rigaya ya bushe"

Ko baya ga zaman mahawarar na kwanaki biyu da zai kawo karshe a wannan Laraba, majalisar za ta sake zama a ranaikun shida da bakwai da takwas na wannan wata inda bayan mahawara za ta kada kuri'a kan kudirin dokar.