1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahawarar karawa Iran takunkumi

September 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuAh

A yau ne wakilan manyan kasashen duniya suka gana a birnin Washinton domin tattauna yiwuwar karawa kasar Iran takunkumi ,adangane da kin watsi datayi da harkokin bunkasa sinadran uranium.Wakilai daga kasashe biyar dake zaunanniyar kujera a komitin sulhu ,da suka hadar da Britani da Sin da Fransa da Rasha da Amurka, ahannu guda kuma da Jamus ne,suka tattauna batun daukan wannan sabon mataki akan Iran.

Rasha da Sin dai sun dai sun bayyana rashin amincewarsu adangane da wannan sabon takunkumi akan Iran,saboda hadin kai da Tehran tayi alkawarin bayarwa hukumar binciken nuclear.