1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahawarar Majalisar Bundestag

October 22, 2004

A mahawarar da tayi a yau majalisar dokokin Jamus ta tattauna shawarar kafa wata cibiya ta tsakiya da zata rika hada kan ayyukan mahukuntan kasar baki daya

https://p.dw.com/p/BvfH

Bisa ga ra’ayin jami’an siyasar jam’iyyun Christian Union akwai bukatar kafa wata cibiya bai daya da zata kunshi kwararrun masana daga dukkan hukumomin tsaron Jamus bisa manufar yaki da ta’addanci. A lokacin da yake bayani wani wakilin ‚yan Christian Union a majalisar dokoki da ake kira Clemens Binninger yayi nuni da cewar wannan cibiya zata iya kunsar kwararru kimanin metan, wadanda zasu rika daukar matakai na musayar bayanai da rahotanni tsakanin kafofi 37 na mahukuntan Jamus. Kazalika ana iya dora musu alhakin bin bahasi ko kuma bin diddigin al’amura da kuma mika bayanai ga mahukuntan da lamarin ya shafa. Amma fa jam’iyyun gwamnatin hadin guiwa ta SPD da The Greens basa marhabin da wannan shawara. Shi kansa ministan cikin gida Otto Schily dan jam’iyyar SPD yana da nasa shirye-shiryen da ya tanada bisa manufa, inda yake fatan ba wa hukumar ‚yan sandan ciki ta Jamus da hukumar tara bayanai ta tarayya cikakken ikon neman dukkan bayanan da suke bukata daga sauran mahukunta na jihohin tarayya. A baya ga haka, an saurara daga karamin minista a ma’aikatar cikin gida Fritz Rudolf Körper yana mai nuna cewar tun da jimawa majalisar dokoki ta Bundestag ta tsayar da shawarar kirkiro wata cibiyar bitar rahotannin da hukumomin leken asiri ke tarawa, kuma cibiyar zata kama ayyukanta a cikin ‚yan watanni kalilan masu zuwa. Amma ma’aikatar cikin gida ba zata amince da kafa wata cibiya ta tsakiya da zata rika hada kan ayyukan hukumomin ‚yan sanda da na leken asiri ba, sai dai kawai a dauki nagartattun matakai na musayar rahotanni tsakaninsu. Gwamnatin hadin guiwa ta SPD da The Greens na kyamar shawarar kirkiro cibiyar ne saboda ta haka ba za a iya fayyace ayyukan da suka shafi mahukunta na ‚yan sanda da kuma mahukuntan leken asiri ba. Su ma ‚yan jam’iyyar FDP na goyan bayan rarrabe ayyukan hukumomin guda biyu, kamar yadda yake kumshe a daftarin tsarin mulkin kasa. Hade kafofin guda biyu karkashin wata cibiya guda daya ta tsakiya zai haifar da rudami da rashin sanin tahakikanin alkiblar da suka fuskanta a game da ayyukansu. Su dai ‚yan Christian Union babban abin dake ci musu tuwo a kwarya shi ne yaduwar wasu masu tsananin kishin addini, wadanda aka kiyasce yawansu zai kai mutum dubu 30 a karkashin kungiyoyi 24 a sassa dabam-dabam na Jamus. A saboda haka take ganin daukar irin wannan mataki zai taimaka wajen hana wadannan masu zazzafan ra’ayin kishin addini samun wata kafa ta sakin jikinsu a nan kasar. A yanzun an danka alhakin bitar lamarin a hannun kwamitin rikon kwarya akan al’amuran cikin gida na majalisar dokokin Jamus, Bundestag a takaice.