1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahmud Abbas ya fara ziyarar aiki a nahiyar turai

March 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5C

Shugaban yankin Palasdinawa, Mahmud Abbas ya isa birnin Vienna na kasar Austria, don fara ziyarar aiki a wasu kasashe a nahiyar turai.

Babban dai batu a lokacin ziyarar shine na kokarin bukatar kasashen,

duba yiwuwar ci gaba da bawa yankin tallafin raya kasa, duk kuwa da kafa gwamnati da kungiyyar masu kishin addinin Islama ta Hamas zata yi.

Kafin dai wannan ziyara, kungiyyar Eu ta bukaci kungiyyar ta Hamas ta kwance damarar yaki sannan a hannu daya ta amince da kasancewar Kasar Israela a matsayin kasa, kafin ta ci gaba da bawa yankin tallafin na raya kasa.

A dai wani lokaci ne a nan gaba ake sa ran Mahmud Abbas zai gana da shugaba Wolfgang Schüssel na Austria, wanda a yanzu haka kasar sa ke rike da shugabancin kungiyyar ta Eu na karba karba.

Bugu da kari ana sa ran kuma, Mahmud Abbas zai gabatar da jawabi a gaban yan majalisar dokokin na Eu dake birnin Strasbourg