1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahmud Abbas ya kira wani taro da nufin dinke baraka da Hamas

June 14, 2006
https://p.dw.com/p/Buu2

Ana ta ƙara samun hauhawar tsamari, a gwagwarmayar da ƙungiyoyin Falasɗinawa na Fatah da Hamas ke yi kan madafan iko, inda a halin yanzu ma, wasu masharhanta ke hasashen matsalar za ta iya taɓarɓarewa, har a kai ga yaƙin basasa. Bayan wata ganawar da ya yi da Firamiyan Hukumar Falasɗinawa Isma’il Haniya, da wakilan sauran ƙungiyoyin Falasɗinun, shugaban Falasɗinawan Mahmoud Abbas ya ba da sanarwar kiran wani taro yau, inda wakilan ɓangarorin Fatah da na Hamas za su tattauna hanyoyin sulhunta rikicin. A birnin New York kuma, babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Kofi Annan, ya bayyana matuƙar damuwarsa game da gwagwarmayar da ɓangarorin Falasɗinawan ke yi da juna kan madafan iko.