1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahukuntan Kenya sun kai samame wurin yin barasa

Pinado Abdu WabaJuly 4, 2015

Wannan samamen ya yi mafari ne, sakamakon yadda shan barasan ya daga wa gwamnatin hankali domin mace-macen da ake dangantawa da shan shi.

https://p.dw.com/p/1FsiF
Kenia Garissa Universität Anschlag Kenias Präsident Uhuru Kenyatta äußert sich zu demAnschlag
Hoto: picture-alliance/dpa/ZUMA Press

Mutane takwas sun hallaka, wasu da dama kuma sun yi rauni sakamakon wani samamen da mahukuntan Kenya suka kai wani wurin da ake yin barasa ba bisa ka'ida ba. Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya rawaito cewa an kama daruruwan mutane an kuma lalata wasu shagunan masu sana'o'i da dama, sanan an zubar da dubban litoci na barasan.

Mahukuntan sun kai samamen ne yankunan da ke tsakiyar Kenya, da babban birnin kasar wato Nairobi inda akalla mutane 80 suka rasu a yayin da wasu da dama kuma suka makance a dalilin wani sinadarin da aka sanya a cikin barasan mai suna Methanol, wanda akan yi amfani da shi ne don hana abubuwa daskarewa a cikin kankara.

Wata jarida mai suna The Star ta ce mutane bakwai daga cikin takwas din sun mutu a cikin wata mota da ke dauke da barasar da aka kwato, inda ake zargi daya daga cikinsu ne ya kunna ashana, a yayinda aka harbe dayan lokacin samamen.