1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mai Koyar Da 'yan Wasan Kwallon-Kafa Na Jamus Yayi Murabus

June 24, 2004

Mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Jamus Rudi Völler yayi murabus daga mukaminsa sakamakon gazawar da kungiyar tayi wajen tsallakawa zuwa zagaye na gaba na gasar cikin kofin kasashen Turai

https://p.dw.com/p/Bvii
Mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Jamus, bayan lallasa kungiyar da aka yi da ci biyu da daya a jiya laraba
Mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Jamus, bayan lallasa kungiyar da aka yi da ci biyu da daya a jiya larabaHoto: dpa

An lura da hali na rudu da rashin sanin tabbas da Rudi Völler, babban mai koyar da ‚yan wasan kwallon kafa na Jamus ya kasance a ciki jim kadan bayan kammala wasan da kungiyar kwallon kafar kasar tayi da ‚yan wasa na kasar Chek, inda aka lallasa su da ci biyu da daya. A cikin hira ta tashar telebijin da aka yi da shi bayan kawo karshen wasan Völler ya ce ko da yake yayi imanin ci gaba da tafiyar da aikinsa har zuwa shekara ta 2006, kamar yadda kwantaraginsa na koyar da kungiyar kwallon kafa ta kasa, ya tanada, amma kuma ba zai makale akan kujerarsa kamar kaska ba. Amma a cikin kasa ta sa’o’i 24 Rudi Völler ya canza ra’ayinsa, inda yayi murabus, saboda a ganinsa, ya gaza kuma ba ya son ya shafa wa kungiyar kwallon kafa ta kasa, kashin kaza sakamakon wannan gazawa tasa. Shi dai Völler mai murabus, an nada shi mukamin koyar da kungiyar kwallon kafa ta kasa ne, sakamakon gazawar da kungiyar tayi wajen kaiwa zagaye na biyu a gasar cin kofin kwallon kafa na kasashen Turai da aka gudanar a kasashen Belgium da Netherlands a shekara ta 2000 a karkashin tsofon mai koyarwa Erich Ribbeck. An shiga doki da murna lokacin da yayi na’am da daukar alhakin koyar da kungiyar kwallon kafar ta kasa baki daya. Amma fa duk wanda yayi bitar yanayin wasannin kungiyar kwallon kafar ta Jamus a cikin shekaru hudun da suka wuce zai ga cewar babu wani ci gaba na a zo a gani da ta samu. Domin kuwa ko da yake kungiyar ta kai wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da aka gudanar a kasashen Japan da Koriya ta Kudu a shekara ta 2002, amma fa ba kwarewa da iya taka kwallo ne suka kai ta ga wannan nasara ba, illa sa’a kawai, saboda kungiyar ba ta fuskanci wasu abokan takara da zasu kalubalance ta ba, sai a wasan karshe inda ta fada hannun ‚yan wasa na kasar Brazil, wadanda suka mayar da ‚yan wasan na Jamus kamar dai ‚yan rakiya ne kawai. Wani abin lura ma shi ne yadda kungiyar kwallon kafar ta Jamus ta ci gaba da gurguncewa tun bayan wasan na cin kofin kwallon-kafa na duniya misalin shekaru biyxun da suka wuce. An lura da mummunan gibin da kungiyar ta Jamus ke fama da shi a gasannin da ta gudanar a kokarin kaiwa gasar karshe ta cin kofin kwallon kafa ta kasashen Turai a kasar Portugal. Babu wata nasara ko sau daya da ta samu akan gaggan kungiyoyin kwallon kafa na ketare. To sai dai kuma murabus din da Rudi Völler yayi daga mukaminsa na mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta kasa ba zai kawo wani banji ga lamarin ba. Domin kuwa a inda take kasa tana dabo shi ne kasar tana fama da karancin kwararrun ‚yan wasa, musamman wadanda zasu iya yi wa sauran ‚yan wasan jagora daga tsakiyar fili. Muddin ba a cike wannan gibi ba to kuwa hatta sabbin ‚yan wasa matasa da ake tinkafo da su, kamar Philipp Lahm da Bastian Schweinsteiger da Lukas Podolski ba zasu iya taimakawa kungiyar ta tsallake zuwa tudun na-tsira ba. Gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya a shekara ta 2006 za a gudanar da ita ne a nan Jamus, kuma a sakamakon haka kasar ta cancanci kaiwa wasannin karshe kai tsaye. Duka-duka wasannin da zata rika shiryawa shi ne na sada zumunci. Watakila hakan zai iya taimakawa magajin Völler akan mukamin koyarwar ya samu kafar gwada ‚yan wasa dabam-dabam har sai yayi katari da nagartattun ‚yan wasan da zasu iya cike gibin da kasar ke fama da shi.