1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maiduguri: Harin bam ya kashe mutane 8

October 12, 2016

Wani harin kunar bakin wake da ake zaton kungiyar Boko Haram ce ta kai da a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno ya hallaka mutane 7 inda wasu da dama suka jikkata.

https://p.dw.com/p/2R9fx
Anschlag in Gombe Nigeria 31.10.2014
Hoto: picture-alliance/dpa

Wanda suka shaida lamarin sun gayawa DW cewar mata ne guda biyu suka tada bam din a tashar Muna a daidai lokacin da ake jiran jami'an tsaro domin jagorantar matafiya zuwa Dikwa da Gamboru da misalin karfe 8:45 na safe. Wani mazaunin birinin na Maiduguri Mustapha Babagana ya ce lokacin da harin ya auku sun kwashi gawawaki 6 da kuma karin wasu mutane da suka jikkata don kaisu asibiti domin yi musu magani. Mutumin ya ce wasu daga cikin wanda suka jikkata din na cikin mawuyacin hali. Wannan dai shi ne karon farko a cikin watanni da dama da aka samu tashin bam a Maiduguri wadda a baya ya sha fama da tada kayar bayan mayakan Boko Haram.