1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Ɗinkin Dunia ta gudanar da kwaskwarima ga dokokin ayukan kwantar da tarzoma

March 16, 2007
https://p.dw.com/p/BuPZ

Majalisar Dinkin Dunia ta rattaba hannu a kan dokar amincewa da gudanar da kwaskarima, ga wasu mahimman ayukan ta guda 2, da su ka jiɓancin kwantar da tarzoma, da kuma kwance ɗamara yaƙi, a ƙasashen da ke fama da tashe-tashen hankula.

Saban sakatare Jannar na Majalisar, Banki Moon, ya gabatar da wannan tsari, wanda ya samu tabaraki daga membobin majalisar mafi rinjaye.

Wajibicin wannan gyaran fuska, ya taso ta la´ akari da kura-kuran da a ka fuslanta a baya wajen ayyukan kwantar da tarzoma, wanda akasari basu cimma nasara ba.

Amma wannan gyara fuska ya,ya ci karo da adawar kasashe kamar su Pakistan da Afghanistan, wanda a halinyan zu, ke daga sahun kasashen da ke cin moriyar ayyukan kwantar da tarzoma.

A jimilce, akwai dakarun shiga tsakani na Majalisar Dinkin Dunia fiye da dubu 10, a sassa daban-daban na dunia.