1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ana bukatar kimanin dola miliyan ɗari don agaza wa al’umman ƙasar Lebanon.

July 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bupd

Babban jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da ba da taimakon agaji, Jan Egeland, ya ce za a bukaci fiye da dola dubu ɗari wajen agaza wa dubban ’yan ƙasar Lebanon, waɗanda suka ji rauni ko kuma farmakin da Isra’ila ke kai wa ƙasarsu tun kwanaki 12 da suka wuce, ya sa suka yi ƙaura daga matsugunansu. Da yake yi wa maneman labarai jawabi a birnin Nicosia na ƙasar Cyprus, kafin ya ƙarasa zuwa yankin Gabas Ta Tsakiya, Egeland, ya ce zai ƙaddamad da wani kira na musamman ga gamayyar ƙasa da ƙasa don a sami taimakon gaggawa ga ƙasar Lebanon din, daga nan har zuwa watannni 3 masu zuwa. A yau ne dai jami’in zai tashi zuwa birnin Beirut don ganawa da mahukuntan ƙasar. A ran talata ne kuma, zai yi shawarwari da shugabannin Isra’ila a birnin ƙudus.