1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce gwamnatin Sudan ta amince bisa manufa da girke dakarun kare zaman lafiyar majalisar a yankin Darfur.

November 17, 2006
https://p.dw.com/p/BubW

A taron ƙasa da ƙasa da aka gudanar kan rikicin yankin Darfur, a birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha, babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan, ya ba da sanarwar cewa, gwamnatin Sudan ta amince bisa manufa, da girke dakarun kare zaman lafiyar majalisar a yankin, waɗanda za su yi aikin haɗin gwiwa tare da dakarun Ƙungiyar Tarayyar Afirka. Amma wakilan gwamnatin Sudan a taron, sun ce sai sun gana da shugabanninsu a birnin Khartoum kafin su ba da tabbacin amincewa da shirin.

Wasu masu sa ido kan yadda ababa ke wakana a yankin na Darfur na ganin cewa, bai kamata a dogara kan sasanta rikicin da ƙarfin soji kawai ba. Marina Peters, shugaban wata ƙungiyar nan Turai, mai nazarin yadda al’amura ke wakana a Sudan, wato „Sudan Focal Point Europe“, ta bayyana cewa:-

„Akwai bukatar sasanta rikici tsakanin al’ummomin yankin da kansu, saboda suna da ɓaraka da yawa tsakaninsu. Kazalika kuma, ’yan tawayen ma na da saɓani tsakaninsu. Amma batun shawo kan barazanar da ƙungiyar nan ta Janjaweed ke yi wa mazauna yankin ne ya fi muhimmanci, saboda su ne ke janyo yawan zub da jinin da ake ta yi a Darfur. Gwamnatin Sudan ta ɗau alkawarin kwance wa ’yan janjaweeed din ɗamara, amma har ila yau babu abin da ta yi game da hakan.“