Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce Iraqi na ta ƙara faɗawa cikin ruɗami da tashe-tashen hankulla.
November 23, 2006Bisa wani rahoton baya bayan nan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta buga, a cikin watan Oktoba da ya gabata kawai, mutane, a galibi fararen hula, fiye da dubu 3 da ɗari 7 ne suka rasa rayukansu a tashe-tashen hankullan da ke ta ƙara haɓaka kamar wutar daji a Iraqi. Ba a dai taɓa samun irin wannan adadin a cikin wata ɗaya kawai ba kawo yanzu. Hare-hare da kashe-kashen da ake ta yi a ƙasar ya sa ɗimbin yawan jama’a na tashi daga matsugunansu, wasu ma na yin ƙaura zuwa ƙasashen ƙetare da ke maƙwabtaka da Iraqin. Majalisar sinkin Duniyar dai ta ƙiyasci cewa, a ko wane wata kusan ’yan ƙasar Iraqin dubu 100 ne ke neman mafaka a Siriya ko kuma Jordan. Gaba ɗaya kuma, tun da aka fara yakin Iraqin, mutane kimanin mmiliyan ɗaya da digo 6 ne suka fice daga ƙasar, inji rahoton.
Game da halin da ake ciki yanzu dai, shugaban Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Iraqin, Gianni Magazzeni, ya bayyana cewa:-
„Tsarin tashe-tashen hankullan ya sake a cikin ’yan watannin da suka wuce. A nawa ganin, mun sami ƙarin tashe-tashen hankulla tsakanin mabiya ɗariƙu ko kuma na ƙabilanci. Ban da haka, akwai kuma hare-haren da aka kai, waɗanda ba ’yan yaƙin gwagwarmaya da ’yan ta’adda kawai ne ke da hannu a cikinsu ba, har da ma gungun ’yan bindiga da kuma na masu aikata miyagun laifuffuka.“