1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Ɗinkin Duniya ta gaza a Kongo

December 1, 2009

Majalisar Ɗinkin Duniya ta gaza a aikin kiyaye zaman lafiya a kewayen tafkin Kongo

https://p.dw.com/p/Kmcs
Shugabar Liberiya Ellen Johnson SirleafHoto: Bettina Ambach

Da farko dai zamu fara ne da wani dogon rahoto da majallar Geo ta gabatar, wadda ke nazarin yadda ake samun ci gaba a fafutukar tabbatar da zaman lafiya a ƙasar Liberiya da kuma yadda mata ke taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da al'amuran ƙasar. Mujallar ta ce:

"Bayan yaƙin basasa na tsawon shekaru 14 Liberiya, sannu a hankali, ta samu kafar farfaɗowa, tana kuma kan hanyar samun dawwamammen zaman lafiya. To sai dai kuma har yau ba tabbas a game da yadda makomar ƙasar zata kasance, saboda da yawa daga manazarta na tattare da imanin cewar ko ba daɗe ko ba jima tsohon madugun 'yan tawaye kuma shugaban ƙasa na da Charles Taylor dake fuskantar shari'a akan miyagun laifuka na yaƙi a kotun ƙasa da ƙasa dake The Hague zai koma gida yana kuma da magoya baya masu tarin yawa duk da zargin miyagun laifuka da ake masa kuma a saboda haka ba wanda ya san abin da zai biyo baya."

A haƙiƙa ba inda majalisar ɗinkin duniya ta gaza kamar a yankin kewayen tafkin Kongo dake ƙuryar tsakiyar Afirka. Domin kuwa sojojinta na kiyaye zaman lafiya a Ruwanda sun kasa taɓuka kome don dakatar da kisan ƙare dangin da dakarun 'yan tsagera na ƙabilar Hutu suka aikata akan 'yan Tutsi, sakamakon umarnin da sojojin suka samu daga shelkwatar majalisar dake birnin New Yoork, in ji jaridar Die Tageszeitung a cikin wani sharhin da ta gabatar ta kuma ƙara da cewar:

"Wani abin kunyar dake faruwa ma, kamar yadda tabbatattun bayanai suka nunar, shi ne yadda ƙasashen majalisar ke wa matakanta na takunkumi zagon ƙasa. Misali ƙungiyar tawaye ta FDLR tana bi ta kan Dubai domin fitar da zinariya zuwa Belgium ta kuma yi amfani da kuɗaɗen don sayen makamai daga Tanzaniya da ƙasashen gabacin Turai. Ƙungiyar kazalika ta kan yi amfani da Jamus wajen halasta kuɗeɗenta, yayinda ita kuma Faransa take karɓar baƙoncin maduguannin 'yan tawaye, sannan Spain da Belgium kuma ke ba da damar hada-hadar kuɗi ga 'yan tawayen".

Deutschland Ignace Murwanashyaka FDLR
Madugun ƙungiyar FDLR Ignace MurwanashyakaHoto: AP

A dai wannan makon aka sake zaman shari'ar wasu madugwannin 'yan tawayen ƙasar Kongo su biyu a kotun ƙasa da ƙasa akan miyagun laifuka dake The Hague ta ƙasar Holland. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi nazarin halin da ake ciki a gabacin ƙasar ta Kongo inda take cewa:

"Ko da yake tun a shekara ta 2002 ne aka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar Kongo a hukumance a Afirka ta Kudu, amma fa har yau ana fama da yaƙi a lardin Ituri mai arziƙin ma'adinai a gabacin ƙasar. Kuma musabbabin rikicin shi ne sabanin dake akwai tsakanin abilar Hema mai goyan bayan asar Ruwanda da Lendu dake samun arin gindin Uganda akan amfani da filaye masu danshi da cin gajiyar albarkatun kasa a yankin".

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu