1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Afghanistan na neman a tsare sojojin Amirka.

May 31, 2006
https://p.dw.com/p/Buw3

Majalisar ƙasar Afghanistan, ta yi kira ga kame waɗanda suka janyo haɗarin da motar sojin Amirka ta yi da motocin fararen hula a birnin Kabul, a ran litinin da ta wuce. Haɗarin dai ya ritsa da a ƙalla mutane biyar, dukkansu fararen hula, har lahira abin da kuma ya haifad da wata mummunar tarzomar da ba a taɓa gani a birnin ba, tun hamɓarad da gwamnatin Taliban da aka yi shekaru 5 da suka wuce. Hukumar rundunar ƙawance da Amirka ke yi wa jagoranci a ƙasar, ta bayyana nadamarta ga haɗarin, inda ta ce lalacewar birkin motar sojin ne ummal aba’isin annobar.

A wata sabuwa kuma, ’yan bindiga sun harbe wasu matan Afghanistan ɗin guda 3, waɗanda ke yi wa wata kungiyar agaji daga ƙasashen Yamma aiki a arewacin ƙasar. Kazalika kuma, wani bam da aka dasa a bakin titi, ya yi bindiga, inda ya halaka ’yan Afghanistan ɗin su biyu, masu yi wa wani kamfanin Amirka aiki a yankin.