1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Bundestag ta amince da tura sojojin Jamus a RDC

June 1, 2006
https://p.dw.com/p/Buvk

Majalisar dokokin Bundestag ta nan Jamus, ta kaɗa ƙuri´ar amincewa, da tura sojoji 780 na ƙasar, a cikin tawagar dakarun ƙungiyar gamayya turai, da za su sa ido, ga zaɓɓukan da za a gudanar a Jamhuriyar demokradiyar Kongo, a ƙarshen watan july na wannan shekara.

Yan majalisar jam´iyun ƙawance na CDU CSU, da kuma SPD, tare da goyan bayan jam´iyar adawa ta The Greens, baki ɗaya, sun bada haɗin kai ga wannan mataki.

Saidai a wata ƙiddidigar jin ra´ayin jama´a, da jaridar Stern, ta gudanar ta bayyana cewar kashi 57, bisa 100 ,na jamasuwa na adawa da tura dakarun su, cikin wannan tawaga.

Daga ayarin sojojin na Jamus, 300 kaɗai,za su zama a Jamhuriya Demokradiyar Kongo, a yayin da sauran za su girka sanani, a ƙasar Gabon, cikin shirin ta kwana.