1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Bundestag ta yi muhawara kan Afganistan

December 4, 2009

Majalisar Bundestag ta tafka muhawara game da makomar aikin da sojojin Jamus ke yi a Afganistan da kuma harin da sojojin nata suka kai a farkon watan Satumba a wannan ƙasa

https://p.dw.com/p/KqPg
Majalisar BundestagHoto: AP

Ko da yake ƙasar nan ta Jamus ba ta bayyanar da ƙarin sojojinta a Afganistan ba, a yammacin jiya Alhamis majalisar Bundestag ta gudanar da muhawara akan wannan ƙasa da kuma harin da sojojin Jamus suka kai a watan Satumba da yayi sanadiyar mutuwar farar hula da dama .

Ministan tsaro, Karl-Theodor zu Guttenberg ya fito fili ya bayyana cewar harin da aka kai kan tankokin mai guda biyu a ƙasar Afghanistan farkon watan satumban da ya wuce, ba abu ne da ya dace a manufofi na soja ba. Ya ci gaba da cewar:

„Zan sake maimaita abin da na faɗa tun farko cewar duk da kasancewar kanar Klein, da ma sauran hafsoshin da suka hallara a wannan zauren, ya ɗauki matakinsa ne domin kare dakarunsa, amma ta la'akari da bayanan dake gabanmu a yanzun, matakin nasa yayi daura da manufofi na soji. Kuma duk da cewar ya zama wajibi in yi gyara a game da bayanin da na bayar da farko, a shari'ance, amma a ɗaya hannun hakan bai shafi fahimtar da nayi wa matakin da kanar Klein ya ɗauka ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa ba zan fita bayan kanar Klein ba“.

Shi kuwa minstan harkoin wajen Jamus, Guido Westerwelle kira yayi da cewa kamata yayi Jamus ta ɗau dabarar janyewa daga ƙasar Afganistan, yana mai kira da a yi aiki don tabbatar da haka tare da nuna muhimmmacin yin nazari akan jawabin da Obama yayi game da sabuwar manufarsa a Afganistan.

"Yace a don haka yana da muhimmaci mu tabbatar cewa abokan haɗin-gwiwarmu sun yi ra'ayi da mu game da haka. Wannan aiki namu muna gudanar da shi ne da nufin tabbatar da cewa Afganistan kanta za ta iya kula da tsaron kanta da kanta. Ba muna gudanar da wannan aiki ne don cimma wani buri namu ba. Muna buƙatar yin aiki akan jadawalin ficewar daga wannan ƙasa sabo da cewa babu wani mahaluki a nan zauren da ke ƙaunar ganin an ci gaba da wannan aiki har illa ma sha'allahu. Muna kuma buƙatar samun goyon bayan wannan majalisa game da aikin da sojojinmu ke yi .

Kakakin jam'iyyar the Green a Bundestag, Jürgen Tritten shi kuma kira yayi da a yi nazari akan aikin da Jamus ke yi a Afganistan inda yace:

"Muna da aiki a gabanmu inda hakan ya sa muka tsawwala aikin da sojojinmu ke yi a Afganistan da shekara guda, kuma za mu iya sauya manufar wannan aiki daidai da sakamakon taron da za a gudanar akan ƙasar ta Afganistan. Saboda haka ne ma har yanzu ba mu iya mun fito da tsarin tafiyar da wannan aiki ba. Ina son na gaya muku cewa majalisar dokokin Bundestag ba ta buƙatar ƙayyade wa'adin aikin da sojojin Jamus ke yi a Afganistan."

Ƙasar Jamus wadda ake sa ran ba za ta ƙara yawan sojojinta a Afganistan ba har sai bayan taron da za a yi a birnin London a watan Janairu, ta lashi takobin haɓaka ƙoƙarin da ta ke yi don kare farar hula a Afganistan.

Mawallafi: Halimatu Abbas

Edita: Umaru Aliyu