1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dattawan Amirka ta albarkaci dokar sayarwa Indiya fasahar nukiliya

December 9, 2006
https://p.dw.com/p/BuYe

Majalisar dattijan Amirka ta bi sahun majalisar wakilai wajen amincewa da wata doka da ta tanadi samun cikakken hadin kai a fannin nukiliya tsakanin Amirka da Indiya. A karon farko cikin shekaru 30 sabuwar dokar ta amince a sayarwa Indiya fasaha da kuma makamashin nukiliya don amfanin farar hula na kasar duk kuwa da cewa har yanzu Indiya ba ta sanya hannu kann yarjejeniyar da ta haramta yaduwar makaman nukiliya a duniya ba. A nata bangaren Indiya zata amince a gudanar da bincike a tashoshinta na makamashin nukiliya. Sakataren kasa a ma´aikatar harkokin wajen Amirka Nicolas Burns wanda a halin yanzu yake wata ziyarar aiki a birnin New Delhi ya bayyana sabuwar dokar da cewa zata karfafa hadin kai tsakanin kasashen biyu.