1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya na daukar matakai a Najeriya

Salissou Boukari
November 18, 2016

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa a kan munin barnar da yakin Boko Haram ya haifar a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, abin da ya sanya kara yawan taimako da take bayar wa a fannin yaki da 'yan kungiyar.

https://p.dw.com/p/2StKy
Mohamed Ibn Chambas
Hoto: AP

Majalisar Dinkin Duniya ta kudiri aniyar taimaka wa mutanen da suka rasa muhallansu a jihar Borno da ke Tarayyar Najeriya, inda ta kara yawan ma'aikatanta a Maiduguri daga 40 zuwa 200. Wakilin musamman na sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kasashen Afrika ta yamma da yankin Sahel Mohammed Ibn Chambas ne ya bayyana haka a Abuja fadar gwamnatin Najeriyar, a ganawar da ya yi da ministan yada labarai da ala'adun gargajiya na kasar a ranar Juma'a 18 ga watan Nuwamba 2016, inda ya bayyana irin yanayin da ya iske yankin, musamman halin da ‘yan gudun hijira ke ciki. 

Mr Chambas ya ce a yanzu Majalisar Dinkin Duniyar ta fara sauya aikin nata daga na taimakon jin kai zuwa ga na sake farfado da yankunan da aka kwato daga hannun Boko Haram. Kimanin mutane miliyan 200 ne dai yakin na Boko Haram ya shafi rayuwarsu a yankin Tafkin Chadi.