1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana samun nasara a yaki da ake da cutar Aids ko Sida

Mohammad Nasiru Awal AS
July 20, 2017

A cikin shekaru kimanin 10 yawan mutanen da cutar mai karya garkuwar jiki ta yi ajalinsu ya ragu matuka.

https://p.dw.com/p/2gtTa
Symbolbild Aids Medikament
Irin yawan magungunan da masu cutar Aids ke sha ke nanHoto: picture-alliance/dpa/J. Kalaene

Yawan mutanen da ke mutuwa sakamakon cutar Aids ko Sida ya ragu da kusan kashi 50 cikin 100 a tsukin shekaru 10 da suka gabata. A cikin wani rahoto da ta wallafa hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da cutar Aids wato UNAIDS, ta ce a bara mutane miliyan daya suka mutu sakamakon kamuwa da cutar mai karya garkuwar jiki. A daidai wannan lokaci kuma yawan sabbin masu kamuwa da kwayoyin cutar ya ragu da mutum miliyan 1.8, sannan a lokaci guda an samu karuwar yawan wadanda ake wa jinya da magungunan HIV. Rahoton ya nuna cewa a shekarar 2016 mutane miliyan 19.5 daga cikin mliyan 36.7 aka yi wa jinya da magungunan na HIV, abin da ke zama na farko wajen samun fiye da kashi 50 cikin 100 na masu dauke da cutar da aka yi wa magani.