1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta fara janyewa daga Eritrea

Hauwa Abubakar AjejeDecember 15, 2005

Saoi 24 kafin waadin da Eritrea ta basu na ficewa daga kasar,Jamian Amurka ,Turai da Rasha sun fara janye jamian su daga Eritrea

https://p.dw.com/p/Bu3N
Jean Marie da yan jaridu
Jean Marie da yan jariduHoto: AP

Cikin halin zaman dar dar a bakin iyaka Eritrea da Habashada kuma tsoron sake barkewar yaki tsakanin makwabtan biyu,kashin farko na dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya 180,sun isa birnin Addis Ababa inda zasu kasance na wucin gadi bayan fatattakarsu da Eritrea tayi.

Mai kula da aiyukan majalisar a Eritrea,Jean Marie Guehenno,yace yanzu suna cikin wani rikitaccen lokaci,bayan kokari da yayi na tsawon kwanaki 3 yana kokarin ganawa da mahukuntan Eritrea da nufin shawo kan mahukuntan Eritrea da su janye batun korartasu.

Jean Marie,ya fadawa manema labarai cewa,halin siyasa da ake ciki yanzu ba abu ne ya suka so ba,inda ya kara da cewa basu taba fuskantar mawuyacin yanayi kamar wannan ba a cikin aiyukansu.

A jiya laraba ne,komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yanke shawarar janye jamian majalisar su 180 da suka fito daga Amurka,Canada,Turai da kuma Rasha biyyowa bayan oda da gwamnatin Eritrea ta bayar na ficewarsu daga kasarta.

Komitin sulhun yayi Allah wadai da wannan umurni,yana mai cewa ba zai karbu ba,ya kuma sabunta bukatunsa na cewa Eritrea ta janye dukkan tsauraran dokoki da ta dorawa maaikatan majalisar,ciki har da haramtwa jirage masu saukar angulu na majalisar yin zirga zirga a kasar.

Shugaban shirin yace,a watan janairu mai kamawa,komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yanke shawara akan mataki da ya kamata ya dauka a game da korar dakarun,bayan ya duba irin illar da korar tayi,wadda akayi imanin itace irinta ta farko da wata kasa ta taba yiwa maaikatan wanzar da zaman lafiya na Majalisar.

Jamian diplomasiya dai sunce,wannan mataki da Eritrea ta dauka,wata alama ce ta nuna bacin ranta ga gazawar kasashe da suka ci gaba a duniya ta matsawa Habasha lamba ta amince da hukunci da aka yanke akan batun kan iyaka a 2002,inda aka mikawa Eritrea garin Badme dake kan iyakarsu.

Kasashen 2 sun gwabza wani mummunan yaki a 1998-2002,wanda yayi sanadiya mutuwar akalla mutane 80,000,haka kuma a yanzu gwamnatin Eritrea tace akwai alamar sake barkewar wani sabon yakin saboda Gwamnatin Habasha tayi watsi da hukuncin da aka yanke na raba kan iyakokinsu.

A dai wata oktoba,komitin sulhu yayi barazanar lakabawa dukkanin kasashen biyu takunkumi,muddin dai sun koma yaki tsakaninsu kuma sunki janye dakarunsu daga bakin iyakarsu.

Ya kuma gargadin lakaba wani takunkumin daban akan Eritrean ita kadai,har sai ta janye sharuddan da ta gindayawa maaikatan majalisar.

Maimakon yin haka sai Eritrean ta fatattaki jamian majalisar,wanda ya tilastawa sakatare janar Kofi Annan tura Jean Marie da mai bada shawara Randir Kumar Mehta don su je su kwantar da hankula.

Bayan sun samu tabbaci daga Habasha na janyewar dakarunta daga bakin iyakar,mahukuntan Eritrea kuwa sunyi watsi da su,suka nuna basu ma san da zuwansu ba.