1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta nemi agaji kan Falasdinawa

Yusuf Bala Nayaya
February 28, 2018

Hukumar ta ce tana son ganin al'ummomin kasa da kasa sun bada tallafin da ya dace don kare hakki da mutuncin 'yan gudun hijirar Falasdinawa.

https://p.dw.com/p/2tSNR
Gazastreifen UNRWA Versorgung Palästinenser
Hoto: picture-alliance/Zuma/A. Amra

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da 'yan gudun hijirar Falasdinawa ta bayyana cewa za ta shirya gangamin neman agajin kudi na musamman a wata mai zuwa a birnin Rome ta yadda za a rage radadin kudaden tallafin da Amirka karkashin Shugaba Trump ta janye kan wadannan 'yan gudun hijira.

Mai magana da yawun hukumar ta UNRWA Chris Gunness, ya bayyana a wannan rana ta Laraba cewa kasar Sweden da Jordan da Masar su za su dauki bakoncin taron da za a yi a birnin na Rome a ranar 15 ga watan Maris.

Gunness ya ce babban burinsu dai shi ne a ga al'ummomin kasa da kasa sun ba da tallafin da ya dace don kare hakki da mutuncin 'yan gudun hijirar Falasdinawa. Hukumar dai ta MDD na ba da tallafi ga Falasdinawa miliyan biyar ne a yankin na Gabas ta Tsakiya.