1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga karin taimako zuwa Pakistan.

October 20, 2005
https://p.dw.com/p/BvOf

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, ya sake yin sabon kira ga gamayyar kasa da kasa da ta kara ba da taimako ga kasar Pakistan, don magance munanan matsalolin da `yan kasar, wadanda girgizar kasar nan ta addaba, ke huskanta. Da yake yi wa maneman labarai jawabi a birnin New York, Kofi Annan, ya kiyasci cewa, kusan mutane miliyan uku ne a halin yanzu suka rasa matsugunansu da duk ababan da suka mallaka, inda ko bargon kare kansu daga sanyi ma ba su da shi, balantana tantin da za su iya kwana a ciki.

A halin da ake ciki dai, Indiya da Pakistan sun amince su bai wa mazauna yankkin Kashmiri damar tsallake iyakar da ta raba wannan yankin da ake ta korafi aknsa. Shugaba Pervez Musharraf na Pakistan ya bayyana cewa, an dau matakin ne, don taimaka wa dimbin yawan mutanen da girgizar kasar da ta auku kwanaki 10 da suka wuce, ta shafa, wadanda kuma ke bukatar taimako cikin gaggawa.

Sabbin alkaluman da jami’an Pakistan din suka bayar dai na nuna cewa, kusan mutane dubu 48 ne suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasar.