1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dokokin EU ta bukaci Wolfowitz yayi murabus

April 25, 2007
https://p.dw.com/p/BuMn

Shugaban Bankin dunia kenan, Paul Wolfowitz, ke neman gafara, ga kuskuren da ya tabka, na biyan albahsi mai toska, ga wata buduwar sa, dake aiki a Bankin Dunia.

To saidai ya zuwa yanzu, wannan neman gafara bai samu shiga ba, a ƙasashen turai.

A game da haka majalisar dokokin ƙungiyar gamayya turai, da ke birnin Stasburg na ƙasar France, ta shirya mahaura ta mussaman a yau laraba.

Yan Majalisar EU, sun yi kira ga shugabar gwamnatin Jamus Angeler Merkel, da ke riƙƘe da matsayin shugabar ƙungiyar gamayyar turai, ta yi iya koƙarin ta, domin cilastawa gwamnatin Amurika, ta janye Paul Wolfowitz daga jagorancin bankin Dunia a sakamakon wannan abun kunya da ya aikata.

Yan majalisar sun yi nuni da cewar, wannan lefi, ya saɓawa matakan yaƙi da cin hanci da karɓar rashawa da banki ta ƙaddamar.

Cemma kamin kiran na EU ƙasashe da ƙungiyoyi da dama na dunia, sun bukaci Wofiwitz ya yi murabus daga mukamin sa.

To saidai har ya zuwa yanzu, ya na ci gaba da samun goyan baya ido rufe, daga shugaban Amurika, Georges Bush.