1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokokin Faransa ta amince da dokar shigara baki kasar

September 20, 2007
https://p.dw.com/p/BuAo

Majalisar dokoki ta kasar Faransa ta jefa kuriar amincewa da wani kudurin doka daya kara matsa kaimi kann dokokin shigar iyalan baki da suke zaune a kasar.Jamiyar dake mulki ta UMP ta samu goyoyn bayan sauran yan majalisa kann wannan batu.Dokar dai ta tilastawa baki da su koyi harshen faransanci tare da bada tabbacin suna da kudi da zasu iya rike kansu kafin su je su zauna da iyalansu.Wannan doka dai ta bukaci yin gwajin kwayar halitta ta DNA don tabbatar da yan uwantaka,kodayake wannan gwaji zaa fara shi ne na wucin gadi kafin dokar ta fara aiki a 2010.