1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokokin Iran ta goyi bayan shugaba Ahmedinejad

January 15, 2006
https://p.dw.com/p/BvC9

Majalisar dokokin Iran ta goyi da bayan matsayin shugaba mai ra´ayin rikau Mahmud Ahmedi-Nijad a game da takaddamar shirin nukiliyar kasar. Shugaban majalisa Gholam Ali Hadad-Adel ya ce majalisar zata goyi bayan dakatar da hadin kan da ake ba hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa idan Amirka da kasashen tarayyar Turai suka yi karar kasar a gaban kwamitin sulhun MDD. Da farko shugaba Ahmedi-Nijad ya yi barazanar cewa zaman lafiyar duniya baki daya ka iya shiga cikin wani hadari, idan kasashen yamma suka mika batun nukiliyar ga kwamitin sulhu. Shugaba Ahmedi-Nijad ya ce kasar sa zata yi amfani ne da fasahar nukiliya a hanyoyin lumana, saboda haka Iran ba ta karya dokokin yarjejeniyar da ta hana yaduwar makaman nukiliya a duniya ba. A gobe litinin jami´an kasashen kungiyar EU da na Amirka da China da kuma Rasha zasu yi wani taro a birnin London akan shirin nukiliyar na Iran. Ana sa rai zasu sanya lokacin da za´a gudanar da wani taron gaggawa na hukumar IAEA.