1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dokokin Jamus ta amince da aikewa da sojojin kasar zuwa Libanon

September 20, 2006
https://p.dw.com/p/Buio
A yau laraba majalisar dokokin Jamus Bundestag ta kada kuri´ar amincewa da tura dakarun kasar wadanda zasu yi aiki karkashin sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD a Lebanon. ´Yan majalisa 442 suka jefa kuri´ar amincewa da girke da dakarun kasar a Libanon, 152 suka nuna adawa da wannan mataki yayin da wakilai 5 suka yi rowar kuri´unsu. Gabanin a kada kuri´ar jam´iyun adawa guda biyu da suka hada da FDP da masu ra´ayin canji sun nuna shakku suna masu cewa ana iya samun artabu tsakanin dakaraun na Jamus da na Isra´ila. Ana ganin haka a matsayin wata matsala musamman saboda tarihin Jamus na ´yan NAZI. Jamus dai ta yi tayin ba da gudunmawar sojoji dubu 2 da 400 da zasu rika yin sintiri a gabar tekun Lebanon don hana yin sumogar makmai ga ´yan Hisbollah.