1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokokin Jamus ta amince da tura dakaru zuwa Lebanon.

September 21, 2006
https://p.dw.com/p/Buih

Farkon tawagar rundunar mayaƙan ruwan Jamus ta fara shirye-shiryen tashi zuwa gaɓar tekun Lebanon, bayan majalisar dokoki ta Bunddestag da ke birnin Berlin, a jiya, ta amince ta tura dakaru dubu 2 da ɗari 4 zuwa yankin, ƙarƙashin laimar dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya. Mayaƙan ruwan dai za su dinga sintiri ne a gaɓar Tekun Lebanon ɗin, wai don hana jigilar makamai zuwa ga mayaƙan ƙungiyar Hizbullahi. Wannan dai shi ne karo na farko da za a girke dakarun Jamus a yankin Gabas Ta Tsakiya. Wata sanarwar da majalisar dokokin ta Jamus ta bayar, ta ce dakarun za su kasance a Lebanon ne har zuwa watan Agustan shekarar baɗi.

A muhawarar da aka yi a majalisar dai, jam’aiyyun adawa guda biyu, wato ’yan FDP, masu sassaucin ra’ayi, da ’yan gurguzu, sun bayyana tantamar da suke yi ga shirin tura dakarun ma gaba ɗaya, inda suke nanata cewa, dakarun rundunar ta Bundeswehr, za su iya kasancewa cikin wani hali, wanda zai iya janyo fafatawa tsakkaninsu da sojojin Isra’ila.