Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta fara zaman ta
October 18, 2005A yau wata guda daidai bayan kada kuri´a, majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta yi zamanta na farko don fasalta kanta. Tare da gagarumin rinjaye na wakilai 614 an zabi dan jam´iyar CDU Norbert Lammert a matsayin sabon shugaban majalisar. Yanzu haka dai dan jam´iyar ta CDU ya maye gurbin dan SPD Wolfgang Thierse. Zaman majalisar a yau ya kawo karshen wa´adin gwamnatin hadin guiwa ta SPD da The Greens, karkashin shugaban gwamnati mai barin gado Gerhard Schröder wanda ya sha kaye a zaben ´yan majalisar dokoki da ya gudana a ranar 18 ga watan satumba. A yau talata ce kuma shugaban tarayyar Jamus Hosrt Köhler zai ba wakilan tsohuwar majalisar zartaswa shahadar kammala aiki. To sai dai har yanzu gwamnatin Schröder ce zata ci-gaba da jan ragamar mulki a Berlin har zuwa lokacin da za´a nada sabuwar shugabar gwamnati, wato Angela Merkel ´yar jam´iyar CDU.