1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokokin Jamus ta fara muhawwara game da girke dakarun kasar a Kongo

May 19, 2006
https://p.dw.com/p/Buxb

Gwamantin tarayyar Jamus ta kare shirin ta na girke dakarun kasar a JDK, shirin da ke shan kakkausar suka daga jam´iyun adawa. A wani jawabi da yayiwa majalisar dokoki ta Bundestag ministan harkokin waje Frank-Walter Steinmeier ya ce Jamus na da kwakkwarar hujjar girke dakarun ta a Kongo. Kasar dai na shirin ba da gudammawar sojoji 780 a karkashin rundunar da kungiyar EU zata tura Kongo don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a lokacin zaben da zai gudana a Kongon a ranar 30 ga watan yuli. Za´a girke wasu daga cikin sojojin ne a yankunan dake kusa da babban birnin kasar wato Kinshasa. A muhawwarar da majalisar dokoki ta fara yau dangane da batun tura sojojin an Bundeswehr a Kongo, ministan harkokin wajen yayi kira ga ´ya´yan majalisar da suka kada kuri´ar amincewa da wannan shiri.

“Idan aka samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kongo, to ko shakka babu yankin gabashin nahiyar Afirka gaba daya zai fita daga wani yanayi na yaki da rikice rikice da kuma wahalhalu iri dabam-dabam da suka addabi al´umar wannan yanki. Saboda haka ya zama wajibi a gare mu, mu amsa kiran Majalisar Dinkin Duniya don tabbatar da tsaro a lokacin gudanar da zaben a ranar 30 ga watan yuli.”

A ranar daya ga watan yuni majalisar dokokin ta Jamus zata kada kuri´a akan wannan batu.