1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dokokin Jamus ta Tattauna Akan Rikicin Kasar Sudan

May 6, 2004

A yau alhamis majalisar dokoki ta Bundestag ta hallara domin tattaunawa akan rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a yammacin kasar Sudan

https://p.dw.com/p/Bvjr
'Yan dudun hijirar Sudan akan hanya zuwa Chadi
'Yan dudun hijirar Sudan akan hanya zuwa ChadiHoto: AP

A lokacin da take gabatar da jawabi ga wakilan majalisar dokokin Jamus ta Bundestag, wadanda suka hallara domin tattaunawa akan rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a Darfur dake yammacin kasar Sudan, ministar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus Heidemari Wieczorek-Zeul ta yi kira da a tura sojan kiyaye zaman lafiya na kasashen Afurka domin dakatar da ta’asar kisan kiyashin dake ci gaba da wanzuwa a wannan yanki. Ta ce lokaci yayi da Kungiyar Karayyar Afurka zata kada wannan runduna ta kiyaye zaman lafiya, sannan ita kuma Kungiyar Tarayyar Turai ta dauki nauyin ayyukansu a kasar Sudan. Bai kamata kungiyoyi na kasa-da-kasa su zauna su harde kafafuwansu suna masu zura ido akan wannan danyyen aiki dake ci gaba da wakana a kasar Sudan ba. Ministar, kazalika bata yi wata-wata ba wajen gabatar da kira ga gwamnati a fadar mulki ta Khartoum da ta dauki nagartattun matakai na dakatar da fatattakar mutane da ake yi daga gidajensu ta kuma ba wa kungiyoyin taimakon jinkai wata cikakkiyar dama domin kai gudummawa ga Bayin Allahn da suka zautu a cikin mawuyacin hali na kaka-nika-yi. a nata bangaren Kerstin Müller, karamar minista a ma’aikatar harkokin wajen Jamus, wacce a gobe juma’a ne idan Allah Ya kai mu zata zarce zuwa birnin New York domin labarta wa kwamitin sulhu na MDD ra’ayinta a game da halin da ake ciki a yammacin Sudan sakamakon tattaunawar da ta gudanar a makobciyar kasa ta Chadi, ta ce ‚yan gudun hijira kimanin dubu 130 da aka yi musu sansanoni a kan iyaka tsakanin Sudan da Chadi suna cikin hali na dardar. Ita ma tayi kira ga kungiyoyi na kasa da kasa da su kara matsin lamba akan gwamnati a fadar mulki ta Khartoum. Ta la’akari da karatowar damina wajibi ne a girmama yarjejeniyar nan ta tsagaita wuta. Ma’aikatar harkokin wajen Jamus zata kara yawan kudaden taimako na ga mutanen dake fama da radadin matakan tsaftace kabila da makiyaya Larabawa ke dauka akan ‚yan-uwansu Musulmi bakar fata a lardin Darfur tare da taimakon gwamnatin Sudan, daga Euro miliyan daya da dubu dari biyar zuwa Euro miliyan biyu da dubu dari biyar. A lokacin hira da jaridar frankfurter Rundschau, Kerstin Müller ta ce muhimmin abu shi ne a yi wa gwamnatin Sudan matsin kaimi domin girmama yarjejeniyar nan ta tsagaita wuta da aka cimma a cikin watan afrilun da ya wuce. Muddin hakan ba ta samu ba to kuwa wajibi ne a fara shawartawa a game da wani nagartaccen mataki na takunkumin da za a iya dora wa kasar Sudan. Muddin ba tashi tsaye aka yi ba al’amura zasu zama gagara badau, sannan su kuma ‚yan gudun hijirar su dada shiga hali na kaka-nika-yi sakamakon karatowar damina. Tun dai abin da ya kama daga watan fabarairun shekara ta 2003 ne ake fama da yakin basasar da yayi sanadiyyar rayukan mutane kimanin dubu goma da kuma tagayyara wasu miliyan daya a yammacin Sudan. Rahotanni da dimidiminsu sun ce an fuskanci arangama tsakanin dakarun sa kai na makiyaya Larabawa da sojan kasar Chadi, inda aka kashe akalla mutane bakwai, shida daga cikinsu farar fula a yau alhamis.