1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dokokin Niger ta gurfanar da ministoci 2 gaban kotu

October 2, 2006
https://p.dw.com/p/BuhZ

Bayan wata da watani na taci ba ta ci ba, a ƙarshe dai majalisar dokoki a Jamhuriya Niger, ta kaɗa ƙuri´ar amincewa da gurfanar da ministocin nan 2, wato Ari Ibrahim da Mounkaila Harouna, da aka samu da hannu dumu dumu, a handamar kuɗin da turawa su ka tallafawa Niger, domin ta kyauatta harakokin makarantu.

Masharanta akan al´ammuran siyasa a Jmahuriya Niger sundauki wannanmataki na Majalisar Dokoki a matsayin wani saban yunkurin na inganta demokraɗiyar da kuma yaƙi da cin hanci da karɓar rashawa, da su ka zama ruwan dare a opisohin gwamnatin kasar , da ke matsayin ɗaya daga ƙasashe mafi talauci a dunia.

Bayan Minista Mounkaila Harouna jiya , yau Majalisar Dokoki ta tsiri kariyar Imunity kokuma Immunite ga Minista Ari Ibrahim, a game da haka ministocin 2 za su gurfana gaban kotun ƙoli ta ƙasa , wada zata yanke masu hukunci da ya dace.

A cewar El Haji Salisu Watsi, ɗan Majalisar dokoki, a ɓangaren jam´iyu masu rinjaye, wannan mataki na matsayin a ba gawa kashi, don mai rai ya ji tsoro, kuma zai ƙara mutunta martabar Majalisar Dokoki ,da wasu ke wa kalon yar amshin shatar gwamnati.