1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Jamus ta zartad da ƙudurin yi wa kafofin tarayya da na jihohi garambawul.

YAHAYA AHMEDJune 30, 2006

Majalisar dokokin tarayyar Jamus ta zartad da ƙudurin yi wa kafofin tarayya da na jihohi garambawul, tare da burin daidaita yadda za a sake rarraba madafan iko tsakanin kafofin, don ka da a dinga samun saɓanin da a wasu lokutan suke kunno kai.

https://p.dw.com/p/BtzU
Angela Merkel na nuna farin cikinta bayan zartad da ƙudurin da majalisar dokoki ta yi.
Angela Merkel na nuna farin cikinta bayan zartad da ƙudurin da majalisar dokoki ta yi.Hoto: AP

Ra’ayoyi dai sun bambanta a kan wannan zaman da majalisar dokokin Jamus ta yi, don zartad da ƙudurin yi wa kafofin tarayya garambawul. Wasu na ganin hidimar kamar wata kyakyawar alama ce ta tarihi. Wasu kuma na ganin, salo ne dai irin na ’yan siyasa, wanda ba ya ƙunshe da komai, sai romon baka kawai. Tsakanin waɗannan ra’ayoyi biyunn ne aka gudanad da muhawara a majalisar. Shugabar gwamnatin tarayya Angela Merkel, ta yi kira ga ’yan majalisar su goyi bayan shirin, a cikin jawabinta:-

„Tsarin kafofin tarayyarmu yana da inganci, kuma ya kafu sosai. Jama’a da dama na jin daɗin kasancewa cikin jihohinsu. Amma bayan fiye da shekaru 60 da kafa tarayyar Jamus, kamata ya yi a yi wa tsarinmu wasu gyare-gyare na kwaskwarima, saboda a halin yanzu, ’yan ƙasarmu da dama ne ke fama da rashin sanin inda aka mai da alƙibla.“

Bisa ƙudurin da aka zartar yau dai, lamarin zai sake. Nan gaba, majalisar tarayya za ta iya zartad da dokoki da dama, ba tare da jiran samun amincewar jihohi ba. Wato a ɗaya ɓangaren, kamar rage wa jihohin angizonsu ke nan. Amma a ɗaya bangaren kuma, su jihohin ne za su dinga zartad da ƙudurorin da suka shafi harkokin ma’aikatan gwamnati, da kare kewayen bil’Adama da kuma sha’anonin ilimi. Wato a nan, an yi ƙoƙarin cim ma wata madafa ne, wadda ta dace da bukatun kafofin tarayyan da na jihohi. Ban da cim ma irin wannan daidaiton, ba za a iya taɓuka komai ba, inji shugaban reshen jam’iyyar SPD a majalisar dokokin tarayya, Peter Struck:-

„Zartad da ƙuduri kann gagarumin batu kamar wannan, ba abu ne mai sauƙi ba. Dole ne mu yarje kan wata madafa tukuna. Saboda biyan bukatun kowa a lokaci ɗaya, ba abu ne mai yiwuwa ba.“

Batun da jam’iyyun gwamnatinn haɗin gwiwar suka yi ta ƙorafi a kansa dai, shi ne na tsarin yaɗa ilimi. Da kyar ne ɓangarorin biyu suka yarje kan cewa, a batutuwan da suka shafi bincike da kimiyya, da kuma kafofin yaɗa ilimi mai zurfi, sai an dama da hukumomin tarayya. Amma abin da ya shafi makarantun sakandare da makamancinsu, jihohin ne kawai za su iya yanke wa kansu shawara, ba tare da kafofin tarayya sun tsoma musu baki ba.

Jam’iyyun adawa dai, sun yi suka ga wasu ɓangarori na ƙudurin. Shugaban jam’iyyar FDP, Guido Westerwelle, ya ce babban kuskure ne a yi wa kafofin kwaskwarima, ba tare da jiɓinta hakan da matsayin tattalin arzikin ƙasar ba:-

„Ba za a iya dai, daidaita tsarin kafofin tarayya da na jihohi, ba tare da tattauna yadda za a samo kuɗaɗen da za a kashe a kansu ba. Sanin kowa ne dai, idan ba a warware wannan matsalar ba, to ba za a iya samun haɗin kai wajen aiwatad da duk abin da aka tsara ba.“

Su dai ’yan majalisar jam’iyyun gwamnati, ba su nuna wata damuwa ga wannan sukar ba. Bugu da ƙari kuma, ƙudurin ba zai fara aiki ba, sai ya sami amincewar majalisar dattijai, wadda ita, a ran juma’a mai zuwa ne za ta yi zamanta don tattauna wannan batun. A nan ma, samun nasarar amincewa da ƙudurin, zai dogara ne kan yawan ƙuri’un magoya bayan shirin da za a samu. Bisa ƙa’ida dai, kashi biyu bisa uku na ƙuri’un ’yan majalisar ake bukatar ƙudurin ya samu, kafin ya zamo dokar da za ta fara aiki.