1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Turai Ta La'anci matakan Bush na Yaki da Ta'addanci

September 12, 2006

A cikin wata sanarwar da ta bayar majalisar Turai tayi Allah waddai da matakan keta hakkin dan-Adam da Amurka ke dauka da sunan yaki da ta'addanci.

https://p.dw.com/p/BtyF
Majalisar Turai
Majalisar TuraiHoto: picture-alliance/ dpa

Gidajen fursuna na sirri da sace-sacen mutane bisa tuhuma da tsauraran matakai na tambayan fursunoni, dukkan wadannan abubuwa ba zasu taimaka a tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a Amurka da sauran sassa na duniya ba. Kazalika ba zasu ba da wata kariya daga ta’asar masu zazzafar akidar addini ba. Wannan shi ne korafin da majalisar Turai tayi akan matakan murkushe ta’addanci da Amurka ke dauka dangane da samun shekaru biyar ga hare-haren ta’addancin da aka kai kan cibiyar ciniki ta kasa da kasa dake a birnin New York. Kantomar majalisar Turai akan manufofin hakkin dan-Adam Thomas Hammarberg yayi nuni da cewar a cikin shekarun da baya-bayan nan an sha sace mutane bisa tuhumarsu kawai, inda aka dinga nuna musu azaba lokacin da ake fuskantarsu da tambayoyi domin su hakikance da laifukan da ake zarginsu da aikatawa. Wannan mataki ya saba da ainifin shikashikan manufofin demokradiyya a cewar sanarwar da majalisar ta Turai mai kasashe 46 karkashin inuwarta ta bayar. Majalisar sai da ta yi suka da kakkausan harshe akan sanarwar da shugaba Bush na Amurka ya bayar makon da ya wuce a game da wasu gidajen kurkuku da hukumar leken asirin Amurka ta CIA ke amfani da su a asurce domin azabtar da fursinoni da keta hakkin dan-Adam. Sakatare-janar na majalisar Terry Davis ya ce wajibi ne a yi biyayya ga kudurorin hakkin dan-Adam na kasa da kasa:

“Ko shakka babu game da cewar wajibi ne shugaba Bush da sauran gwamnatocin kasashen Turai su kare lafiyar al’ummominsu, domin ita kanta nahiyar Turai tana fuskantar barazana. Wajibi ne wadannan gwamnatoci su shiga farautar mutanen da ake kyautata zaton kasancewarsu ‘yan ta’adda a cafke su a kuma yanke musu hukunci. Amma abin da fahimta ba shi ne me yasa za a tafiyar da wannan mataki a wasu gidajen kurkuku da aka tanadar a asurce. Matakan da Birtaniya ta dauka sun banbanta da wannan. A lokacin da wasu ‘yan ta’adda suka yi yunkurin dana bom a cikin wani jirgin sama dake kan hanyarsa ta zuwa Amurka ‘yan sandan Birtaniya sun cafke su suka kuma fuskancesu da tambayoyi, amma ba a asurce ba.”

Majalisar Turai tayi kira ga hukumar leken asirin Amurka ta CIA da ta dakatar da dukkan matakan da ta rika dauka a shekarun da suka wuce na sace mutanen da ake tuhuma da kasancewa ‘yan ta’adda da fuskantarsu da tambayoyi a asurce. Shi kuma sakatare-janar na majalisar yayi kira ga kasashen dake karkashin inuwarta da su rika bin diddigin ayyukan hukumomin leken asirin kasa na ketare da na cikin gida. Bai kamata a bar wa ‘yan sanda da sojoji da hukumomin leken asiri alhakin tafiyar da matakan yaki da ta’addanci ba. Shi ma tuntubar juna da shawarwari da musayar ra’ayoyi akan al’adu da addini wani muhimmin mataki ne na kandagarkin zaffan ra’ayin akida da tashe-tashen hankula, a cewar sanarwar ta majalisar Turai.